Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin shan ruwa isashe barazana ce babba ga lafiyar ‘dan adam: Abubakar Muhammad Isah

Published

on

 

 

  • Yawan shan ruwa mai yawa zafi na Da mahimmanci ga lafiyar dan adam/
  • Rashin shan ruwan na haifar da matsaloli ga lafiyar ‘dan adam
  • Matsalolin sun hadar da bushewar fatar jiki da dai sauransu

 

Wani jami’in lafiya a asibitin kashi na Dala a Jihar Kano Abubakar Muhammad Isah ya ce ‘yawan shan ruwa mai yawa musamman a wannan lokaci na zafi yana da matukar mahimmanci a jikin ‘dan adam’.

Abubakar Muhammad Isah ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio da safiyar yau, wadda tattaunawar ta mayar da hankali kan muhimmancin shan ruwa a lokacin zafi.

Ya kuma ce, ‘rashin shan ruwa na haifar da bushewar fata da daskarewar jinni da dai sauransu’.

‘Haka zalika rashin ruwa a jikin ‘dan adam kan jawo masa matsaloli da dama ciki harda bushewar fatar jiki da dai sauransu.

Abubakar Muhammad Isah ya kuma ce ‘a lokuta da dama idan mutum yana jin ba dadi a jikinsa, yasha ruwa sosai zai ji ya samu lafiya.

 

 

Rahoton:Nura Bello

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!