Labarai
NDLEA ta kama dan kasar Chadi da ake zargin yana safarar kwayoyi ga Boko haram
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wani mutum dan asalin kasar Chadi mai suna Adama Oumaru Issa wanda ake zargin yana safarar miyagun kwayoyi ga kungiyar boko haram.
Mutumin mai shekaru talatin da biyar an kama shi ne a garin Jalingo da ke jihar Taraba.
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi, ya ce, binciken su na farko ya gano cewa, mutumin dillali ne da ya kwarance wajen safarar miyagun kwayoyi ga ‘yan boko haram da ke bakin daga.
A cewar sa, wanda ake zargin ya kuma sayo kwayoyin ne a garin Onitsha da ke jihar Anambra, inda ya boye su cikin jakar mata.
Ya kuma ce dubun sa ya cika ne a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta kai miyagun kwayoyin ga ‘yan boko haram.
You must be logged in to post a comment Login