Labarai
NDLEA ta kama sama da kilo 490.7 na tabar wiwi da sauran kayan maye a Sokoto

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA a Jihar Sokoto ta kama kilo 490.7 na tabar wiwi da kwalabe 17,568 na Codeine a jihar Sokoto.
Kwamandan rundunar a jihar, Mustapha Gidado, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin taron manema labarai a Sokoto.
Ya ce jami’an NDLEA sun kama kwali 54 na Codeine, yayin da jami’an Hukumar Kwastam suka tare kwali 198 a kan hanyar Illela, inda jimillar ya kai 236 dauke da lita 756.8 na ruwan.
Ya kara da cewa an kama tabar wiwin ne cikin buhu 47 a dakin wani Monday Effiong da ke zaune a yankin Tamaje a Sokoto.
Kwamandan ya bayyana cewa an kama wanda ake zargi tare da kayayyakin kuma za a gurfanar da shi a kotu, yana mai cewa kamen ya biyo bayan bayanan sirri daga wani ɗan kishin kasa.
You must be logged in to post a comment Login