Labarai
NDLEA za ta fara yi wa yan hidimar kasa gwajin shaye-shaye

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta bayyana cewa za ta fara yi wa matasa ‘yan hidimar kasa da kuma masu shirin yin aure gwajin tu’ammali da miyagun kwayoyi nan ba da jimawa ba.
Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya, ne ya bayyana hakan lokacin ganawarsa da Darakta Janar na hukumar NYSC Janar Olakunle Nafiu.
Ya ce an dauki matakin ne domin rage shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Haka kuma, Buba Marwa ya ce, ba wai an dauki matakin ne don hukunta wadanda aka samu suna tuma’ammali da kayan maye ba ne, illa kawai kokarin yi musu magani domin kare lafiyarsu.
Ya ce kuma ce, daya daga cikin hanyar da suke ganin za a iya kawo karshen matsalar ita ce yi wa ‘yan hidimar kasa gwaje-gwajen.
You must be logged in to post a comment Login