Labarai
NEC ta bayyana damuwa kan yadda ake yawan satar ma’adinan Najeriya

Majalisar Tattalin Arzikin Kasa Najeriya watau National Economic Council NEC, ta bayyana damuwa kan yadda ake yawan satar ma’adinan kasa irin su Zinare da sauran albarkatun ƙasa ba bisa ka’ida ba.
Majalisar ta ce, ana yin hakan ne ta hanyar hakar ma’adinai ba tare da izini ba, sannan ana fitar da su zuwa ƙasashen waje, ba tare da komai ya shiga asusun gwamnati ba.
Rahotonni sun nuna cewa, wannan matsala na kawo babbar asara ga tattalin arzikin ƙasar, tare da rage yawan kudaden shiga da gwamnati ke iya samu daga sashen ma’adinai.
Majalisar ta bukaci hukumomi masu ruwa da tsaki da su tsaurara matakan tsaro a wuraren da ake hakar ma’adinai, tare da tabbatar da cewa duk wanda ke da hannu a wannan haramtacciyar sana’a an gurfanar da shi a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login