Connect with us

Labarai

NEF ta buƙaci shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci don magance matsalar tsaro

Published

on

Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya NEF ta buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a yankin sakamakon matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara wanda ya lalata rayuka da tattalin arzikin ƙasar.

 

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere ya fitar, ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan hare-hare da garkuwa da mutane da kashe su ba ƙaƙautawa da ake ci gaba da yi a yankin.

 

Ƙungiyar ta kuma buƙaci “Gwamnati ta bayar da diyya da agaji ga waɗanda lammuran matsalar tsaro suka shafa ciki har da waɗanda suka rasa matsugunansu.”

 

Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan da suka haɗa da ƙarfafa tsaron iyakoki, da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe makwafta cikin ƙungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka domin magance ayyukan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke ta’adi kan iyakoki, da kuma haɗa kai da ƙungiyoyin ƙasashen waje kamar Majalisar ɗinkin duniya domin samun tallafi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!