Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ni da kaina naje EFCC ba kamani suka yi ba-Kwankwaso

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, shi da kan sa ya miƙa kan sa ga ofishin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a ranar Lahadin da ta gabata.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan radion Nasara a ranar Laraba, a wani ɓangare na bikin cikarsa shekaru 65 a duniya.

Kwankwaso ya ce “ranar da na je ofishin EFCC ba’a gudanar da aiki ma, amma saboda da na girmama doka da kuma hukumar ya sa na je kuma na amsa tambayoyin da hukumar ta yi min ba tare da an samu matsala ba”

“Kun san halin maƙiya da kuma masu sharri suna ta yaɗa labarin wai an kamani, wanda kuma ba haka ba ne kawai suna so su ɓata min suna”.

Kwankwaso ya ci gaba da cewa “Lokacin da na ji sanarwar hukumar ta EFCC ta ke na fara shirin zuwa domin na amsa tambayoyin da za su yi, wanda kuma na yi bayani kan zargin da ake a kai na wai na ci kuɗin ma’aikatan hukumar fansho ta jihar Kano”.

Wannnai dai na zuwa ne bayan da wasu rahotanni suka nuna cewa hukumar EFCC ta kama tsohon gwamna Kwankwaso akan zargin da ma’aikatan hukumar fansho na Kano suka gabatar.

A yau Alhamis ne Rabiu Musa Kwankwaso ya cika shekara 65 a duniya kuma ya tabbatar da cewa zai yi amfani da ranar wajen kaddamar da makarantar gyaran hali a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!