Ƙetare
Niger: Malaman makaranta sun janye yajin aikin da suka tsunduma

Malaman makaranta a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da janye yajin aikin da suka tsunduma a farkon makon nan da muke ciki.
Janye yajin aikin dai ya biyo bayan kawo karshen takun saka da aka kwashe tsawon lokaci ana yi tsakanin gwamnatin milkin soji a jamhuriyar ta Nijar da malaman makarantar kan batun biyan bashin da suke bin gwamnatin.
A ranar laraba ne dai ɓangarorin biyu suka cimma matsaya, lamarin da ya sa malaman janye yajin aikin da suka tsunduma a farkon mako wanda ya kasance karo na 4 a jere.
An dai kwashe tsawon lokaci ana tattaunawa, inda gwamnatin ta amince zata biya muhimman buƙatun malaman, ciki har da ɗaukan ma’aikata na din-din-din, hakazalika ta amince da biyansu alawus alawus da suke bi ta hanyar basu filaye domin a cewar gwamnatin, bata da isassun kudin da zata iya biyan bashin ma’aikatan
Sai dai kungiyoyin malam sun ce a shirye suke su koma yajin aikin sai baba ta gani idan har gwamnati ta saɓa alƙawuran da ta ɗauka.
You must be logged in to post a comment Login