Connect with us

Manyan Labarai

Nijar: Bazoum ya kama hanyar lashe zaɓe

Published

on

Sakamakon baya-bayan nan da aka fitar a zaɓen shugaban jamhuriyar Nijar zagaye na biyu ya nuna cewa Bazoum Muhammad dan takarar jam’iyyar PNDS tarayya ne akan gaba da kuri’u fiye da miliyan biyu.

Yayin da abokin takarar sa na RDR chanji Mahamman Usmane ke da kuri’u sama da miliyan daya da dubu dari biyar.

Mahamman Ousmane ya samu yawan kuri’u ne a jihohin Yamai da Tilaberi yayin da shi kuma Bazoum ya sami nasara a jihohin Tahoua da Zinder da Diffa da kuma Maradadi.

A ranar Lahadi aka gudanar da zaɓen zagaye na biyu, inda aka fafata tsakanin manyan ƴan takarar biyu.

Ana sa ran bayyana sakamakon nan ba da jimawa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!