Connect with us

Labarai

Nijar ta mayar da ƴan gudun hijirar Najeriya 153 gida

Published

on

Najeriya ta karɓi ƴan gudun hijirar ƙasar 153 daga Jamhuriyar Nijar a wani yunkuri na tabbatar da dawowarsu cikin aminci da daraja.

Ofishin hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA reshen Kano ne ya karɓi waɗannan ƴan gudun hijira tare da haɗin gwiwar Hukumar ƴan gudun hijira ta ƙasa NRC da hukumar ba da agajin gaggawa ta SEMA, da rundunar tsaro ta NSCDC.

Ƴan gudun hijirar sun isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:50 na tsakar daren Talata ta jirgin Sky Mali Airline.

Bayan kammala rajista da hukumar shige da fice ta Najeriya NIS, an kai su makarantar horarwar hukumar domin gudanar da cikakken bincike da tantancesu tare da dukkan masu ruwa da tsaki.

An gudanar da tantancewar a ranar 27 ga Janairu, 2026, inda bayanan ƴan gudun hijirar suka nuna cewa akwai maza manya 46, mata manya 37, yara maza 38 da kuma yara mata 32.

Hadin gwiwar duk masu ruwa da tsaki ya tabbatar da cewa aikin tantancewa ya gudana cikin tsari, nasara, kuma ba tare da wani matsala mai hatsari ba.`

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!