Connect with us

Labarai

NiMet ta yi hasashen samun mamakon Ruwa mai dauke da Iska da tsawa

Published

on

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi hasashen samun tsawa da Iska hadi da ruwan sama mai karfi a sassan kasar nan daga yau Litinin zuwa Laraba mai zuwa.

 

Hukumar ta kuma ce, ana sa ran samun tsawa mai hade da ruwan sama kadan a wasu sassan jihohin Taraba da Kebbi.

 

Daga baya kuma, za a samu tsawa da matsakaicin ruwan sama a sassan Arewa maso Gabas da jihar Kaduna, Taraba da Kebbi.

 

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta ce za a samu tsawa da ruwan sama kadan a wasu sassan Jihar Neja, yayin da yamma ake sa ran samun tsawa da matsakaicin ruwan sama a mafi yawan yankin.

 

A yankin kudu kuwa hukumar ta yi hasashen samun gajimare, tare da yiwuwar samun tsawa da ruwan sama kadan a wasu sassan jihohin Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!