Connect with us

Labarai

Hukumar NIHSA ta yi gargadi kan yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a Najeriya

Published

on

Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Najeriya NIHSA, ta yi gargadin cewa akwai yuwuwar a samu ambaliyar ruwa a yankuna sama da dubu Takwas da ke fadin kasar a makon nan da muka shiga.

 

Haka kuma, hukumar ta ce, makarantu dubu 4,500 a jihohi 15 na iya fuskantar barazanar ambaliyar ruwan suma.

 

Hukumar ta ce tashin ruwan koguna na iya haifar da ambaliya a wuraren da ke da rauni, lamarin da ka iya shafar makarantu, asibitoci, kasuwanni, wuraren ibada da gonaki.

 

Jihohin da gargadin ya shafa sun hada da Imo, Cross River, Delta, Ebonyi, Benue, Anambra, Akwa Ibom, Edo, Enugu, Bayelsa, Kogi, Abia, Taraba, Rivers da Lagos.

 

Daraktan-Janar na hukumar, Arch Umar Mohammed, ya bukaci gwamnatocin jihohin da abin ya shafa su gaggauta kwashe mutanen da ke zaune a wuraren da ke fuskantar hadarin ambaliyar Ruwan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!