Connect with us

Labarai

Gwamnatin Zamfara ta yi wa ma’aikatan lafiya ƙarin albashi na kaso 95

Published

on

Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin albashin ma’aikatan lafiya da kashi casa’in da biyar cikin ɗari.

 

Sabon tsarin albashin ya fara aiki tun daga ranar bakwai ga watan Satumban 2026, inda aka tsara shi bisa tsarin albashin ma’aikatan lafiya da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi.

 

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Zamfara, Shehu Baraya, ne ya bayyana hakan a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Satumba, 2026.

 

Ya ce ƙarin albashin wani ɓangare ne na sauye-sauyen da gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ke yi domin inganta harkokin kiwon lafiya da kuma walwalar ma’aikatan lafiya a jihar.

 

Gwamnatin ta bayyana cewa ƙarin albashin zai taimaka wajen ƙarfafa ma’aikatan lafiya, da kuma samar da kyakkyawan yanayin aiki domin inganta harkokin bayar da kiwon lafiya ga al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!