Labarai
NIWA ta sanya dokar hana zirga-zirgar kwale-kwale marasa lasisi a fadin kasar nan

Hukumar da ke kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa a Nijeriya (NIWA) ta sanya dokar hana zirga-zirgar kwale-kwale waɗanda ba su da lasisi da kuma lodi a wuraren da ba su da izinin yin hakan, a wani mataki na daƙile yawan haɗurran jiragen ruwa tare da kare rayukan al’umma a faɗin ƙasar.
Babban daraktan hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
A cewarsa, daga yanzu ba za sake barin wani kwale-kwalen fasinja da ake biyan kuɗi ya yi lodi a tasha ko wurin da NIWA ba ta amince da shi ba.
Kazalika ya jaddada cewa dole ne a bayyana sunayen dukkan kwale-kwale da kuma wuraren da suka yi lodi, yayin da su kuma masu gudanar da zirga-zirgarsu dole su samar da kuma tilasta yin amfani da rigunan kariya a ko yaushe.
NIWA ta sanya dokar hana yin lodi daga dukkan wuraren da ake yin lodin da ba sansu ba ko kuma ba su da izinin yin haka a faɗin ƙasar nan, ba za a bari wani kwale-kwale ya ɗauki fasinja ko ya yi lodi daga kowane wuri da NIWA ba ta amince ko kuma ta yi wa rajista ba,’’ a cewar Oyebamiji.
Matakin hakan dai ya biyo bayan wasu munanan hatsarin kwale-kwale da suka afku a watannin baya-bayan nan Nijeriya.
You must be logged in to post a comment Login