Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki bisa karancin kudi da tsadar Fetur

Published

on

Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi barazanar tafiya yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, sakamakon karancin kudi da tsadar man fetur da suka addabi mutane ke fama da su.

Shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan zaman tattaunawar da kungiyar ta gudanar kan halin da ma’aikata ke ciki saboda tsadar man Fetur da kuma karancin kudi.

Ya ce kungiyar za ta gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, idan har gwamnati ta gaza magance matsalar karancin kudi da kuma wadata ‘yan Nijeriya da man fetur, daga nan zuwa wa’adin da kungiyar ta diba, to za su dauki mataki na gaba na tsunduma yajin aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!