Kasuwanci
NNPC : ba za a iya ci gaba da sayar da man fetur akan N162 ba
Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC) Malam Mele Kyari ya ce a duk wata kamfanin na kashe naira biliyan dari zuwa dari da ashirin wajen biyan tallafin man fetur.
Malam Mele Kyari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa ta Asorok da ke Abuja.
Wannan na zuwa ne a lokaci guda da ake tada jijiyar wuya kan ikirarin da gwamnatin shugaba Buhari ta yi na cewa ta daina biyan tallafin mai.
Shugaban kamfanin na NNPC ya kuma ce a gaskiyar lamari ba za su iya ci gaba da sayar da mai akan farashin naira dari da sittin da biyu ba.
‘‘ A yanzu haka ana shigo da tataccen mai ne akan naira dari biyu da talatin da hudu amma ake sayarwa akan naira dari da sittin da biyu, a don haka sauran gibin NNPC ne ke biya’’ a cewar Malam Mele Kyari
You must be logged in to post a comment Login