Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Babu sha’irin da zai yi wakokin yabo a Kano sai yana da ID Card – Afakallah

Published

on

Hukumar tace fina-finai dab’i ta Jihar Kano ta kaddamar da shirin bayar da katin shaida wato ID Card ga masu waken yabo wato sha’irai na Jihar Kano.

Shugaban hukumar Alhaji Isma’il Na’Abba Afakalla ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin, yana mai cewar wannan wani mataki ne na tsaftace harshen sha’iran yayin waken yabo a Jihar Kano.

Wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar Hassan Mukhtar Abubakar ya fitar yau, ta ce shugaban majlisar sha’iran Jihar Kano Malam Sidi Abba ya alkawarta cewa mambobin kungiyarsa za su martaba wannan tsari na hukumar ta tace fina-finai da dab’i ta Jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!