Coronavirus
NNPC ta tallafawa Kano da kayan yakar Coronavirus
Kamfanin man fetur na kasa NNPC da abokan hurdarsa sun baiwa jihar Kano tallafin kayan aiki domin yakar cutar Covid-19.
Kayayyakin da suka bayar sun hada da na’urorin shakar iska da kayan kariya na jami’an lafiya da sauran kayayyaki.
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya karbi kayayyakin a fadar gwamnatin Kano, inda ya mika su ga shugaban kwamitin tattara tallafi da rage radadi ga al’umma kan annobar Covid-19 Farfesa Yahuza Bello.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito mana cewa karamin ministan man fetur na kasa Timipre Marlin Sylva tare da shugaban NNPC Mele Kyari ne suka jagoranci tawagar kawo tallafin.
Har ila yau, tawagar tayi alkawarin cewa za ta ginawa jihar Kano asibitin yaki da cutuka masu yaduwa.
A nasa bangaren gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi godiya da irin gudummuwar da suka kawowa jihar Kano a lokacin da take tsananin bukatar taimako.
You must be logged in to post a comment Login