Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kananan hukumomin Kano sun shirya yakar COVID 19

Published

on

Kungiyar shuganannin kananan hukumomi na jihar Kano ta ce kananan hukumomi a matakin su, sun shirya tsaf don tunkarar annobar Covid-19, la’akari da yadda ta ke yaduwa a fadin duniya.

Shugaban karamar hukumar Nasarawa Alhaji Lamin Sani wanda kuma shine shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta jihar kano ya bayyana hakan ta cikin shirin barka da hantsi na nan Freedom Radiyo wanda ya mayar da hankali kan shirin da kananan hukumomi suka yin a dakile yaduwar Corona virus a nan jihar Kano.

Lamin Sani yace kananan hukumomin jihar Kano sun yi tanadin kayayyakin aiki da kuma aikin wayar da kan mutane akan cutar ta covid 19.

Ya kuma ce Kananan hukumomin na kokari wajen ganin an tsaftace muhalli da kuma tabbatar da cewa jama’a na tsaftace hannayen su domin hana cutar samun muhalli a jihar Kano.

Ya kuma yi kira ga mutane da su baiwa yunkurin gwamnati na hana shigowar wannan cuta jihar Kano hadin kan da ya dace, da kuma yin biyayya ga shawarwarin likitoci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!