Labarai
NNPC ya sanar da shirinsa na fara hakar rijiyar Mai a Jihar Nassarawa
- Kamfanin Mai a Nijeriya zai fara hakar rijiyar mai a Jihar Nassarawa.
- Shugaban Kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan.
- Anasa ran fara hakar rijiyar man a watan Maris din shekarar 2023.
Kamfanin mai Nijeriya NNPCL ya sanar da shirin hakar rijiyar mai na farko a jihar Nassarawa.
Shugaban Kamfanin, Malam Mele Kyari, ne ya bayyana hakan yayin da Gwamnan Jihar, Engineer Abdullahi Sule, ya jagoranci wata tawaga ta fitattun ‘yan asalin Jihar Nassarawa a ziyarar ban girma da suka kaiwa kamfanin NNPC a Abuja.
Kyari, ‘ya ce sakamakon binciken da aka gudanar ya tabbatar da kasancewar albarkatun iskar carbon mai yawa a jihar Nasarawa’.
A watan Maris din shekarar da muke ciki ne ta 2023 ake sa ran za a fara aikin hakon man.
By:Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login