Connect with us

Labarai

Gobara ta hallaka ma’aikatan NNPC 7 a garin Benin

Published

on

Wata gobara da ta tashi a kamfanin mai na kasa NNPC ta yi sanadiyyar mutuwar ma’aikatan kamfanin guda 7, a tasharsa da ke Benin a Jihar Edo.

Shugaban sashen yada labarai na kamfanin Kennie Obateru ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja, inda ya ce gobarar ta auku ne a ranar talata.

Kennie Obateru ya shaida cewa tuni aka fara binciken musabbabin faruwar gobarar, kuma sun sanar da dukkan bangarorin da suka dace a kai.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban kamfanin man na NNPC Mele Kyari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!