Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Jigawa Golden Stars ta kai banten ta da kyar

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden stars , ta kai banten ta da kyar bayan doke abokiyar karawarta Kwara United a gasar Firimiya ta kasa mako na ashirin da uku.

Wasan wanda aka fafata a filin wasa na Sani Abacha dake unguwar Kofar mata, Kwara United ce ta fara shiga gaban Jigawa Golden stars, da Kwallo inda dan wasa Chinedu Onyelenu, a minti na 45, ana dab da za’a tafi hutun Rabin lokaci ya sa Kungiyar sa a gaba.

Bayan dawowa zagaye na biyu, dan wasan Jigawa Dogara Peter ya rama wa kungiyar sa Kwallo a minti na 78, sai Samuel Stone da Kwallo ta biyu a minti na 90 na wasan da ya baiwa kungiyar ta Jigawa nasarar samun maki uku.

A ta bakin mai horar da kungiyar ta Jigawa, Gilbert Opana, yace zasu cigaba da kokari tare da yin duk mai yiwuwa domin ganin sun kare martabar kungiyar ta hanyar zama a cikin gasar ba tare da komawa zuwa rukuni na biyu ba.

Labarai masu alaka.

Kungiyar Kwallon kafa ta Jigawa Golden stars ta lalasa Wikki Tourist

An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu

Shima a nasa bangaren , mai horar da kungiyar Kwara United Ashifat Sulaiman, yace ya gamsu da busar alkalin wasa, a hannu daya kuma zasu duba kura- kuran su don tunkarar sauran wasannin da zasu fafata a gaba.

A dai gasar firimiyar ta kasa, can a birnin Makurdi, Kano Pillars ta samu damar yin biyu da biyu da mai masaukin baki Lobi Stars , a wasan da aka buga a filin wasa na Akper Aku dake birnin Makurdi .

‘Yan wasan Lobi Carlos Galeya da Samad Kadiri a mintuna na takwas da 18, suka saka kungiyar su a gaba da kwallayen inda Samad Kadiri ya zura tashi da bugun daga kai sai mai tsaron raga wato Penalty , a nata bangaren Pillars ta biya bashin kwallayen ta hannun dan wasanta Auwalu Ali Malam daya zura kwallayen a mintuna na Arba’in da biyu da sittin da takwas, wanda hakan yasa aka tashi wasa 2 da 2.

A sauran wasannin gasar firimiyar da aka fafata sun hada da

DAKKADA 1-0 HEARTLAND

MFM 0-0 ENUGU RANGERS

NASARAWA 3-0 KATSINA UTD

RIVER UTD 0-0 FC IFEANYI UBA

SUNSHINE STARS 1-0 ABIA WARRIORS

WIKKI T 0-1 PLATEAU UTD

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!