Connect with us

Labaran Wasanni

NPFL: Za a dawo ranar 6 ga watan Disamba

Published

on

Za a dawo ci gaba da gasar cin kofin kwararru ta Najeriya wato NPFL na kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 a ranar 6 ga watan Disamba.

Yayin da kamfanin dake shirya gasar ya fitar da jadawalin wasannin, kungiyar kwallon kafa ta Enyimba za ta karbi bakuncin Abia Warriors a ranar farko bayan an dawo.

Enyimba dai ta sha lashe gasar tare da daukar kofin har sau takwas a baya.

A rana ta biyu kuma Kwara United za ta karbi bakuncin Aba Elephants a garin Ilorin dake jihar.

Kamar yadda kamfanin dake shirya gasar ya wallafa, za a kawo karshen gasar a ranar hudu ga watan Yulin shekarar 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!