Kiwon Lafiya
NUC:zata fara nazartar manhajar jami’oin Najeriya don bunkasa koyo da koyarwa
Hukumar kula da jam’io ta kasa (NUC) ta ce ta fara nazartar manhajar jami’oin kasar nan da nufin bunkasa harkokin koyo da koyarwa.
A cewar hukumar sake fasalin manhajar zai bai wa dalibai da suka kammala karatu a jami’oin kasar nan kwarewar da za su rika gogayya da takwarorinsu na kasashen duniya.
Shugaban hukumar ta NUC Farfesa Abubakar Rasheed ne ya bayyana haka a wajen bikin yaye dalibai karo na bakwai a wata jami’a mai zaman kanta da ke Abuja.
Ya ce gwamnati ta damu matuka kan yadda kamfanoni da hukumomi ke korafi game da rashin kwarewar dalibai da suka kammala karatu a jami’oin kasar nan.
Farfesa Abubakar Rasheed wanda wani darakta a ofishin babban sakatare Mr Chris maiyaki ya wakilta, ya ce, kwamitin na karkashin jagorancin tsohon shugaban hukumar ta NUC ne Farfesa Peter Okebukola.
Ya kuma ce, kwamitin na aiki dare ba rana don ganin an samar da manhaja ta bai daya da za ta da ce da zamanin da ake ciki