Connect with us

Labarai

NUPENG ta dakatar da yajin aiki bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote

Published

on

Ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta shirya bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote Refinery kan ’yancin mutane na kafa ƙungiya.

Wanne na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da NUPENG ɗin ta fitar a shafinta na X.

Cimma matsayar ya biyo bayan ganawa ta musamman da hukumar DSS ta kira, tare da halartar Ministan Kuɗi, Wale Edun, da shugabannin NLC da TUC.

A cikin yarjejeniyar da aka sanya hannu, an amince cewa ma’aikatan kamfanin da ke son shiga ƙungiya za su samu damar yin hakan, tare da fara tsarin nan take da kuma kammala shi cikin makonni biyu.

a cewar yarjejeniya, babu wani ma’aikacin Dangote da za zalunta saboda sanarwar yajin aikin.

Da wannan matsaya, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa, yayin da ɓangarorin biyu za su koma wurin Ministan Ƙwadago bayan mako guda domin bayar da rahoto

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!