Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NVBF an gayyaci ‘yan ƙwallon Volley 14 zuwa sansanin daukar horo

Published

on

Hukumar ƙwallon Volley ball ta Najeriya ta gayyaci ‘yan wasa daga rukunin matasa ‘yan kasa da shekaru 19 zuwa 20, sansanin daukar horo a Kaduna.

Najeriya zata fafata a wasannin share fage na gasar kofin Duniya ‘yan 19 da na ‘yan kasa da shekaru 21, na ƙwallon Volley ball ta yashi a birnin Phuket , na kasar Thailand daga ranar 06 zuwa 19 ga Disamba 2021.

A sanarwar da jami’in yada labaran hukumar ta Volley ball Famous Daunemigha , ya fitar ta ce ‘yan wasan tuni sun shiga sansanin horo a Kaduna da zai kai su har zuwa ranar 02 ga Disamba 2021, karkashin mai horar dasu John Iwerima da mataimakiyar sa Christy Amadi.

Daga cikin ‘yan wasan sun hada da ..

Maza matasa ‘yan kasa da shekaru 21, Ahmed Abdulrasheed (Niger ), Emenike Collins (Nigeria Police), Chidebere Okeke (Nile), Safa Collins (Edo ), Babalola Hussain (Plateau ) sai Sunday Jubril.

Mata ‘yan kasa da shekaru 21: Tyokaa Doom (Benue ), Ifeoma Mordu (Delta ), Aishat Abdulraheem (Kwara ) and Ndukyaba Kelechi (Niger ).

Mata ‘yan kasa da shekaru 19: Naomi Yaro (FCT Abuja ), Esther Mbah (FCT), Rita Amadi (New Generation’ Port Harcourt) da Sarah Ali (Plateau ).

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!