Labarai
Obasanjo ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar sarkin Zazzau
Ya yin da ake cigaba da zaman makoki a jihar Kaduna bisa rasuwar marigayi mai martaba Sarkin Zazzau Dr, Shehu Idris a ranar Lahadin da ta gabata ‘yan uwa da abokan arziki na ciki da wajen kasar nan na cigaba da yin tururuwa don yin ta’aziyyar a fadar sa.
Sarkin ya rasu ne a asibitin sojoji na 44 dake Kaduna bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 84.
A yayin addu’ar kwanaki 3 da rasuwar marigayin da safiyar yau Laraba shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana marigayi Mai martaba Sarkin Zazzau Dr, Shehu Idris da cewa mutum ne mai gaskiya da rikon Amana.
Shima gwamnan jihar Kaduna Mal Nasir Elrufai da yake jawabi a wajen adduar uku ta Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Dr Shehu Idris y ace jihar Kaduna ta yi babban rashi kasancewar marigayi sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris mutum ne mai son zaman lafiya da cigaban jihat ta Kaduna.
Wakilin mu na Kaduna Bababngida Abdullahi ya rawaito cewa, Gwamnan jihar Kaduna Mal Nasiru Elrufa’I na cewa jihar Kaduna ba zata taba mancewa da irin gudunmawar da sarkin na Zazzau ya bayar bag a jihar da ma kasa baki daya.
You must be logged in to post a comment Login