Labarai
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya yi gargaɗi kan yiwuwar harin ta’addanci

Ofishin jakadancin Amurka da ke kasar nan ya gargaɗi ‘yan kasarm kan yiwuwar harin ta’addanci da ka iya shafar cibiyoyin ta da kuma makarantu masu alaka da ƙasar a fadin Najeriya.
A sanarwar da ofishin jakadancin da ke Abuja ya fitar, an buƙaci ‘yan Amurka su ƙara yin taka-tsantsan idan za su ziyarci ofisoshin diflomasiyyar Amurka ko kuma cibiyoyin da ke da alaka da kasar.
Sanarwar ta ambaci ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Legas, inda aka buƙaci ‘yan kasar su kasance cikin lura tare da ɗaukar ƙarin matakan tsaro idan za su je waɗannan wurare.
Haka kuma ta shawarci ƴan ƙasar da su guji cunkoson jama’a ko zanga-zanga, sannan su sake duba tsare-tsaren tsaron kansu tare da iyalansu.
You must be logged in to post a comment Login