Kiwon Lafiya
Ofishin uwargidan shugaban kasa ya fitar da sanarwa kan kame babban dogarinta
Ofishin Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ya fitar da wata sanarwa da yayi karin haske kan kamawa tare da tsare babban dogaron mai dakin shugaban kasa Sani Baban-Inna da ya aikewa jaridar Premium Times
Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai ga Uwargidan shugaban kasa Suleiman Haruna da ya sanya wa hannun kan cewar an ja hankali Hajiya Aisha Buhari ne bayan da wani rahoto ya mamaye kafafen yada labarai a jiya da shafukan sada zumunta cewa ta bada umarnin a tsare babban dogarin ta saboda zargin aikata zamba cikin amince da yayi wajen amfani da sunan ta.
Sanarwa ta kara da cewar ba ita ce ta bada umarnin ba rundunar ‘yan sanda ta kasa ita ce ta kama tare da tsare Sani Baban-Inna don gudanar da bincike saboda zargin sa da ake yi na karbar kudade a hannun wasu mutane da sunan Aisha Buhari.
A cewar sanarwar tun a shekara ta 2016 ne Sani Babban-Inna yake rike da wannan mukamin na babban dogarin ta, sai dai abun takaicin shi ne yadda bincike ya nuna, yana zambatar mutane kudade da sunan Uwargidan shugaban kasar.
A don haka ne Hajiya Aisha Buhari ta ce zata yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga al’umma bata taba aikar wani ko kuma ma’aikacin ta wajen wani don karbar kudi a madadin ta da iyalan ta ba.
Akan haka duk wanda ya san ya baiwa Sani Baban-Inna kudi toh kada yayi kasa a gwiwa yaje ya karbi kudin sa, don kuwa Uwargidan shugaban kasa ba zata karfafawa wani ko wata wajen yin zamba cikin amince ba.