Labarai
Operation Puff-Adder sun farwa ‘yan bindiga dadin na Ansaru a dajin Koduru a Kaduna
Jami’an tsaron kasar nan na musamman na Operation Puff Adder da ke karkashin rundunar ‘yan sandan kasar nan sun farwa ‘yan bindigar nan na Ansaru da ke cikin dajin Koduru a birnin Gwarin Jihar Kaduna, inda suka kashe ‘yan ta’adda sama da 250.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan kasar nan DCP Frank Mba ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce tun da sanyin safiyar jiya laraba ne dakarun na su na musamman suka fara barin wuta kan ‘yan bindigar a maboyarsu ta dajin Küduru da ke Birnin Gwari.
Frank Mba ya kara da cewa matakin ya zama wajibi la’akari da irin munanan ayyukan yan bindigar a yankunan Jihohin arewacin kasar nan da ya yi Kamari a baya-bayan nan, inda sace-sacen mutane da garkuwa da su suka kara ta’azzara.
To sai dai rundunar yan sandan ta tabbatar da cewayan bindigar sun samu nasarar harbo jirginta na sama mai saukar Ungulu da ke taimakawa yan sandan wajen tarwatsa yan bindigar, bayan da suka yi amfani da bindigogi masu harbor jirgin sama, inda ya fado kasa.
DCP Frank Mba ya bayyana cewa direban jirgin da mai taimaka masa sun yV kokari matuka wajen yin saukar gaggawa a barikin sojojin sama da ke Kaduna ba tare da wata gagarumar fangarda ba.
Daga nan ne aka garzaya da su asibiti don ba su kulawar gaggawa kuma suna nan babu wani mummunan rauni a jikinsu.
Babban sufeton yan sandan kasar nan Muhammad Adamu ya jinjinawa jami’an na sa bisa irin kwazo da suka nuna, inda ya sha alwashin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.