Kiwon Lafiya
Oyo:yan sanda sun yi sanidayar makanta wani matashi
Wani matashi Samuel Ogundeji ya rasa idanun sa bayan da aka yi zargin cewa sashin yaki da fashin da makami na rundunar ‘yan sanda ta kasa dake Yankin Saki a jihar Oyo ya azabtar da shi.
Kimanin shekaru 2 ke nan da aka zargi sashin yaki da fashi da makami na rundunar ‘yan sanda da azaftar da Samuel Ogundeji.
A cewar Iyayen matashin sun iyakacin kokarin su don ganin idanuwan sa sun dawo garai amma abun ya gagara, kasancewar asibitoci daban-daban dake Ilori babban birnin jihar Kwara da kuma wasu asibitoci dake kan iyakar kasar nan da jamhuriyyar Benin sun tabbatar da cewa ya rasa idanun sa.
Da yake bada labarin yadda ya rasa idanun sa,Samuel Ogundeji ya ce a ranar 10 ga watan Janairun bara ne ya nemi aiki a wani mashaya dake Saki bayan da ya samu aikin ne akan Naira dubu goma kowanne wata, daga bisani kuma wata matashiya daga cikin ma’aikata ta ajiye aikin ta, ganin haka sai aka maida ni aiki cikin otel din baki daya