Labarai
PDP Kwankwasiyya ta nemi Aminu Wali ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa
Jam’iyyar PDP a nan Kano ta gayyaci ɗaya daga cikin jagororinta Ambasada Aminu Wali domin ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.
A wata sanarwa da shugabancin jam’iyyar na mazaɓar Hotoron Kudu ya fitar, ta ce, ana zargin ambasadan da yiwa jam’iyyar zagon ƙasa a don haka aka gayyace shi domin ya zo ya kare kan sa.
Da yake karin bayani a kai, Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar Kano, Bashir Sanata ya ce, ɗaukar wannan mataki ya zama dole, la’akari da zarge-zargen da suke yiwa ambasada Walin.
Sanata ya ce, ana zargin Ambasada Aminu Wali da ƙin bai wa jam’iyyar gudunmawa a zaɓen 2019.
Na biyu kuma yana mu’amala da Gwamnatin jam’iyyar APC a Kano, ta yadda baya iya yin hamayya da ita.
Sai dai har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto, tsagin Aminu Wali bai ce komai ba a kan lamarin.
You must be logged in to post a comment Login