Connect with us

Labarai

Ana wata-ga-wata: PDP ta dakatar da Ambasada Aminu Wali

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen mazabar Hotoro ta kudu ta dakatar da tsohon ministan kasashen wajen kasar nan Ambasada Aminu Wali daga jam’iyyar na tsawon watanni shida.

A cikin wata takarda da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugaba da sakatare na jam’iyyar a mazabar ta Hotoro ta kudu, ta ce, ta dau wannan mataki ne sakamakon gaza bayyana gaban kwamitin da jam’iyyar ta kafa akansa.

A cewar jam’iyyar gazawa da Ambasada Aminu Wali ya yi na bayyana gaban kwamitin jam’iyyar don kare kansa game da zargin da ake yi masa, ya sanya ta ga ba ta da zabi da ya wuce ta dakatar da shi har na tsawon watanni shida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!