Connect with us

Labarai

PDP ta yi Alla-wadai bisa hari da sace daliban makarantar Sakandaren Maga

Published

on

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa makarantar Sakandaren yan mata ta gwamnati da ke Maga, a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, inda ’yan bindiga suka sace dalibai 25 tare da kashe mataimakin shugaban makarantar.

A wata sanarwa da PDP ta fitar, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Ini Ememobong, ya bayyana damuwa kan ci gaba da tabarbarewar matsalar tsaro a wasu sassan Najeriya.

Jam’iyyar ta zargi gwamnatin Tarayya da gaza daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa, ta na mai cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali kan siyasa maimakon tsaro.

PDP ta mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, tare da kira ga gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su dauki mataki na gaggawa, musamman ganin irin yawan sace-sacen da ke faruwa a jihohin Nasarawa da Plateau da Kano da kuma Katsina a baya-bayan nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!