Connect with us

Labarai

PDP ta zargi APC da daukar matakan da ka iya jefa dimokuraɗiyya cikin hatsari

Published

on

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana damuwa tare da zargin wasu matakan da jami’yar APC ke ɗauka a baya-bayan nan inda ta ce hakan na iya jefa dimokuraɗiyya cikin haɗari.

 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Ini Ememobong ya fitar, PDP ta ce abubuwan da ke faruwa na nuna alamun shirye-shiryen murƙushe jam’iyyun adawa,  a babban zaben mai zuwa na shekara 2027.

 

Sanarwar ta zargi jam’iyyar mai mulki ta APC da ƙoƙarin lashe zaɓe ta kowace hanya, ko da hakan zai kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya da kuma zaman lafiya a  kasar nan.

 

PDP ta kuma nuna damuwa kan yadda wasu manyan hukumomi na ƙasa, ciki har da Hukumar Zabe ta kasa INEC musamman yadda take  tafiyar da wasu al’amura da suka shafi jam’iyyun siyasa.

 

 Jam’iyyar ta ce sabuwar sanarwar INEC kan batun shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark ta ƙara tayar da hankali a ƙasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!