Labarai
PDP ta zargi shugaba Tinubu da wuce Gona da Iri a Rivers

Jam’iyyar adawa ta, PDP, ta yi zargin cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya wuce iyakokin da kundin tsarin mulki ya ba shi, bayan da ya dakatar da Gwamnan jihar Rivers, Siminilayi Fubara, a lokacin dokar ta-baci da aka ayyana a jihar.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa dakatar da gwamna a yayin dokar ta-baci ya sabawa tanade-tanaden tsarin mulkin ƙasar nan, wanda bai bai wa shugaban ƙasa damar tsoma baki kai tsaye wajen rushewar doka da oda a jihohi ba.
A cewar jam’iyyar, matakin shugaban ƙasa ya kawo cikas ga tafiyar dimokuraɗiyya a Najeriya, inda ta yi kira gare shi da ya nemi afuwa daga ‘yan ƙasa kan abin da ta bayyana a matsayin kuskure mai girma.
PDP ta kuma yi gargadin cewa irin wannan mataki na iya zama barazana ga kwanciyar hankali da zaman lafiya a sauran jihohi, musamman idan aka bari aka yi amfani da shi a matsayin abin koyi a gaba.
You must be logged in to post a comment Login