Kiwon Lafiya
PDP:Ta Kira taron gaggawa don tauna batutuwan zabe
Jam’iyyar PDP ta kira wani taron gaggawa domin tattana batun dage zabukan kasa da hukumar zabe ta kasa INEC ta yi a makon jiya.
Taron wanda ake saran za a gudanar da shi yau Talata a birnin tarayya Abuja, shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus ne zai jagoranta.
Mai Magana da yawun jam’iyyar Mr Kola Ologbondiyan, ya ce za a gudanar da taron ne domin sake nazartar shirye-shiryen da jam’iyyar ta yi kan zabukan kasa.
A cewar sa kwamitin gudanarwar jam’iyyar ne zai gudanar da taron a sakatariyar jam’iyyar da misalin karfe goma sha biyu na ranar yau.
Haka zalika ya kara da cewa shugabannin jam’iyyar za su kuma tattauna kalaman da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan masu satar akwatunan zabe a yayin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC jiya a Abuja.