Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kano Pillars za ta biya tarar sama da naira miliyan 7 – LMC

Published

on

Kamfanin dake shirya gasar League ta kasa LMC, ya ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars naira miliyan 7 da dubu dari 5 bisa tada hargitsi da magoya bayansu suka yi.

A ranar Lahadin data gabata ne 13 ga watan Yuni, aka zargi magoya bayan Pillars da tada hargitsi yayin da kungiyar take wasa da Akwa United a cigaba da gasar League ta kasa a jihar Kaduna.

LMC ta ce Pillars za ta biya tarar naira miliyan 5 bisa karya dokar dakile yaduwar cutar COVID-19, sai kuma tarar naira miliyan 2 da dubu dari 5 kan tayar da hargitsi da magoya bayan kungiyar suka yi, lamarin da ya saka aka tashi daga wasan ba tare da an kammala ba.

Haka zalika, an dai karkare wasa ne da safiyar ranar Litinin 14 ga watan Yuni.

LMC ta kuma yi barazanar cire maki 3 a cikin makin da Pillars ta samu, matukar hakan ta sake faruwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!