Labarai
PSC ta ƙi amincewa da karin girma ga masu muƙamin ASP 179

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta Najeriya PSC ta ki amincewa da karin girma ga mataimakan Sufiritan rundunar ‘Yan sanda ASPs guda 179.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta PSC, Ikechukwu Ani ya fitar, ta tabbatar da cewa, 176 daga cikin jami’an da abin ya shafa sun riga sun yi ritaya, yayin da guda uku kuma daga ciki tuni sun rasu.
Sai dai ya ce, an ƙara wa jami’an ASP guda 952 girma zuwa mukamin mataimakan sufiritanda watau DSP.
Hukumar ta kuma ki amincewa da karin girma ga wasu jami’an da bata bayyana adadin su ba wadanda ta ce, sam ba su cancanta inji sanarwar.
You must be logged in to post a comment Login