Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Qatar 2022: Kasar Masar ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta

Published

on

Hukumar kwallon kafar kasar Masar ta sallami mai horar da tawagar ‘yan wasan kwallon kafar ta, Hossam Al-Badry sakamakon ci 1-1 da kasar ta yi da Gabon.

Egypt dai ta buga wasan neman tititin buga gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a kasar Qatar a shekara mai kamawa ta 2022 a jiya Lahadi.

 

Hukumar kwallon Afirka CAF ta dakatar da wasan Guinea da Morocco
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar kwallon kafar kasar ta fitar ga manema labarai a yau Litinin 06 ga Satumbar shekarar 2021.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumar kwallon kafar kasar ta Masar ta godewa mai horarwar tare da abokan aikin sa kan aikin da su ka yi na jan ragamar kasar.

Kazalika sanarwar ta ce nan da awanni 48 kasar za ta bayyana sabon mai horarwar da zai ci gaba da jan ragamar kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!