Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Qatar 2022: Sai kasar Portugal ta buga wasan Playoff za ta samu tikitin buga gasar

Published

on

Dan wasa Cristiano Ronaldo da ke wasa a kasar Portugal zai fuskanci tsaikon buga wasan Playoff domin samun damar zuwa gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a Qatar.

Kasar Portugal dai ta yi rashin nasara a wasan da suka buga da kasar Serbia a ranar Lahadi 14 ga Nuwambar 2021.

Portugal wadda ta yi rashin nasara a wasan da ci 2 da 1.

Tin da fari dai kasar Portugal ce ta fara zura kwallon farko a mintuna na 2 ta hannun dan wasa Renato Sanchez.

Kana a mintuna na 33 dan wasan Tudan ya warware kwallon da aka zura musu a wasan.

Sai dai dab da za a kammala wasan a mintuna na 90 dan wasa Miteovic ya kara kwallo ta biyu da hakan ya bawa kasarsa ta Serbia nasara a wasan da ci 2 da 1.

Yanzu haka dai a rukuni na A kasar Serbia itace ke mataki na farko da maki 20.

Sai kuma kasar Portugal da ta ke a mataki na biyu a rukunin da maki 17 a wasanni 8 da suka buga.

Sai dai yanzu haka kasar Portugal za ta jira buga wasan karshe na Playoff domin samun damar kai wa cikin jerin kasashen da zasu buga gasar kofin duniya a shekara mai zuwa ta 2022 a kasar Qatar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!