Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Dani Alves ya sake komawa Barcelona

Published

on

Dan wasan bayan kasar Brazil Dani Alves ya sake komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelon a matsayin kyauta.

Hakan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da Kungiyar ta Barcelona ta fitar a ranar Juma’a

Alves wanda a yanzu zai ci gaba da wasa a tsohon filin wasan kungiyar da ya bari na Camp Nou.

Mai shekaru 38 zai fara daukar horo a kungiyar a mako mai zuwa, sai dai bazai fara buga wasa ba har sai watan Janairu mai zuwa.

Dani Alves dai na guda daga cikin manyan ‘yan wasan baya a duniya ya bar tawagar da akewa take da Blaugrana a shekarar 2016.

Kafin daga bisani ya koma PSG kana ya koma Sao Paulo, inda a yanzu kuma yayi kome zuwa filin Camp Nou.

A tsahon shekaru takwas da ya shafe a Barcelona a baya, ya buga wasanni 391 da zura kwallo 23.

Inda kuma ya lashe gasanni akalla 23 a kungiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!