Addini
Rabon kwana ke kawo tabarbarewar aure a arewacin Najeriya – Malami
Limamin masallacin Usman Bin Affan da ke Gadon Kaya a nan Kano ya bayyana matsalar rabon kwana ga ma’aurata da cewa shi ne babbar kalubalen da ma’aurata ke fuskanta a rayuwar zamantakewar su ta yau da kullum.
Sheikh Ali Yunus ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radiyo da ya mayar da hankali kan zamantakewar aure.
Ya ce, a shari’ance dare ne kwana ba rana ba, kamar yadda aka fi gani a wasu gidajen aure wajen rabon kwana, yana mai cewa ya danganta da yadda ma’auratan suka amince da rabon kwana a tsakanin su.
Ya kara da cewa, wajibi ne mutum yayi adalci tsakanin iyalansa akan rabon kwana tare da sauke nauyin zamantakewar aure kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Shaeikh Ali Yunus ya ja hankalin ma’aurata musamman maza da su tabbatar sun daidaita tsakanin matayen su wajen yin adalci wanda hakan zai basu damar tashi a gobe kiyama da cikakken jiki.
You must be logged in to post a comment Login