Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rage kudaden haraji shizai bunkasa tattalin arziki – Ahmad Rabi’u

Published

on

Tsohon Kwamishinan ciniki, masana’antu, kasuwanci, ma’adanai, jami’iyyun gama kai da yawon bude ido na jihar Kano, Alhaji Ahmad Rabi’u, ya bukaci Gwamnatoci a matakai daban-daban na kasar nan, da suyi duba kan matakan bunkasa tattalin arziki biyo bayan nakasu da aka samu sakamakon annobar cutar COVID-19.

Alhaji Ahmad Rabi’u ya bukaci gwamnatin tarayya dana jihohin kasar nan da su ragewa ‘yan kasuwa da kamfanoni harajin da ake cajar su, a wani mataki na farfado da tattalin arzikin kasa da ya samu nakasu a dalilin annobar cutar COVID-19.

Alhaji Ahmad Rabi’u wanda ke zaman mataimakin shugaban cibiyar ciniki ta kasa, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da wakilin Freedom Radio Umar Idris Shuaibu.

Ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta dai-daita yanayin da harkokin kasuwanci da ciniki za su ci gaba da gudana cikin sauki.

“Yanayi mai kyau ya hada da zaman lafiya da tabbatuwar tsaro, ka’idoji na haraji na Gwamnati za su taimaka wajen kawo bunkasa da gudanuwar tattalin arziki yadda ya kamata”. A cewar Ahmad Rabi’u.

Tsohon Kwamishinan ya ce la’akari da yadda masana’antu suka rage kayayyakin da suke samarwa, shakka babu yanayin ya taba al’umma da dama, wajen gaza biyan ma’aikatansu albashi yayinda wasu suka rasa ayyukansu dungurumgum.

Ya kara da cewa, akwai bukatar Gwamnati da sauran hukumomi su kara kaimi, wajen baiwa al’umma tallafi a harkokin sana’oin su.

“Bada bashi da babu ruwa zai taimakawa al’umma su farfado daga yanayin da aka samu kai na annobar COVID-19”.

Ahmad Rabi’u ya kara da cewa kafin zuwan wannan annoba, tuni Gwamnatin Kano tayi aiki tukuru wajen dai-daita yanayin kasuwanci, ta yadda jihar zata yi gogayya da takwarorinta irin su Lagos da sauran birane da suka shahara ta fuskar kasuwanci a kasashe daban-daban na Afrika.

Tsohon Kwamishinan kasuwancin a zangon Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje na farko, ya kuma ja hankalin al’ummar jihar Kano dama kasa baki daya, wajen nuna halin juriya da sanin ya kamata a cikin rayuwarsu, ta yadda za su taimaki Gwamnatoci a tsarikan da za su bullo da su na tallafa musu.

Alhaji Ahmad Rabi’u ya tabbatarwa al’ummar yankin sa na  Dambatta dama jihar Kano baki daya, wajen ci gaba da bada gudunmawarsa a duk wani abu da zai ciyar da su gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!