Labarai
Rahoto : An ceto wani tsoho da ya shafe shekaru 30 a daure a Kano

A baya-bayan nan dai hukumomi a nan Kano sun ceto mutane uku da aka daure tsawon shekaru a gida ba tare da samun kyakykyawar kulawa ba.
Tun a shekarar 2019 da ta gabata ne, Freedom Radio ta fara bankado rahoton wani magidanci da ya daure ‘ya’yan sa biyu a daki tsawon shekaru wanda har hakan ya yi sanadiyyar rasuwar daya daga ciki.
Haka kuma kamar yadda kuka ji tun a farkon shirin rundunar ‘yan sanda ta sake kubutar da wani tsoho da ya shafe shekaru talatin cikin sasari a rufe a yankin karamar hukumar Rogo dake nan Kano.
Ku saurari rahoton wakilin mu Abubakar Sabo a cikin labarun Freedom Redio
You must be logged in to post a comment Login