Labarai
Rahoto : An rufe gidan da ake saida abincin Naira 30 a Kano
Daga Abubakar Tijjani Rabi’u
Tsadar kayan masarufi ta sanya rufe gidan abincin Naira Talatin a nan Kano, wanda a kwanakin baya al’umma kanyi tururuwa zuwa don ciki cikin su a naira Talatin.
Mamallakin gidan abincin, mai suna, Alhaji Haruna Injiniya, ne ya tabbatar da hakan a wata ziyara da Freedom Radiyo takai masa a safiyar yau.
A zantawar Freedom Radiyo da Alhaji Haruna Injiniya, mazaunin unguwar Sani Mainagge A ya ce tsadar kayan abinci ce ta sanya su rufe gidan abincin, sabo da a yanzu kudin kayan abincin da suke siya ya ninka yadda suke siya a baya.
Ya kuma ce duk da mutanan da suke zuwa siyan abincin basuji dadin hakan ba kuma suma basu so hakan ba duba da yadda ake taimakwa wadan da basu dashi.
Ya kuma yi kira ga gwamnati data kawo musu dauki wajen tallafa musu don ci gaba da gudanar da sana’ar tasu duba da yadda ake taimakawa wadan da basu dashi.
Wasu daga cikin mutanan da suke zuwa siyan abincin na naira Talatin a gidan sun bayyana yadda sukaji.
Hakan ce ta sanya muka tuntubi wani mai awoh kayan abinci, mai suna Shamsuddin Sale, donjin yadda kayan abinci yake a yanzu da kuma yadda yake a baya.
Idan mai sauraro zai iya tunawa a shekarar data gabata ne ministan Noma Sabo Na Nono ya ce za’a iya cin abinci akan naira talatin a kano kuma mutun ya koshi sanadiyyar matsin lamba da al’umma sukaiwa gwamnatin tarayya kan tsadar kayan masarufi a Najeriya, wanda hakan ne yasa Alhaji Haruna Injiniya Bude gidan a bincin nasa a wancen lokaci.
You must be logged in to post a comment Login