Rahotonni
Rahoto : Dalilan da suka sanya Buhari zai ciyo bashi a kasashen waje
Daga Fatima Muhammad Adamu
A kwana kwanan nan ne, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnatinsa ta rika ciwo bashi daga kasashen ketare matukar ana son magance matsalar da kasar nan ke fama dashi.
Wanda ya kara da cewa duk matsin da ake fama dashi kasar nan bazai iya kawo karshen shiba, dole sai da cin bashi.
Wannan jawabi na Shugaban kasa dai ya janyo cece-kuce tsaknain al’ummar kasar nan yayin da wasu ke ganin duk da ciyo bashin da gwamnatin ke yi amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Sai dai duk hada Muhammadu Buhari a nasa bangaren ya dage kan cewa zai yi amfani da kudaden wajen gudanar da ayyukan raya kasa
Haka zalika yace kudaden shigar da kasar nan ke samu bazai kai ayi amfani dashi ba wajen kawo karshen matsalar da ake fuskanta a kasar nan.
Freedom radio ta tattauna da wasu mutane a nan Kano don jin ra’ayoyinsu akan wannan lamari.
“A gaskiya bai dace a halin da ake ciki Buhari ya ciyo bashi ba, ya yin da wani ke cewa ana kara dorawa Najeriya nauyi ne kawai”
Haka Zalika Freedom Radio ta tattauna da wani Malami a sashen nazarin tattalin arziki a jamiar tarayya da ke Dutsen jihar Jigawa, Dr Ahmad Garba Khali, kan wannan batu.
A hannu guda kuma, mun tuntubi babban mai taimakawa shugaban Kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu kan wannan lamari, wanda ya bayyana cewa kudaden da suke hannun gwamnati ba zasu biya bukatun ‘yan Najeriya bas hiya gwamnati ke ranto kudade don gudanar da ayyukan raya kasa.
Malam Garba shehu ya kara da cewa babu wata gwamnatin da za ta zo a kasar nan sannan ta iya biyan bukatun al’umma, musamman a wannan lokaci irin wannan ba tare da ranto kudi ba.
You must be logged in to post a comment Login