Labarai
Rahoto: Jama’ar unguwa na gina wa kansu kwalbati ta kusan miliyan 5 a Kano
Al’ummar wasu unguwanni a nan birnin Kano sun yi haɗin gwiwa wajen sake sabinta kwalbatin da ta haɗa yankunansu.
Unguwannin sun haɗar da Darma da Dukawa da Zangon bare-bari da kuma wani ɓangare na unguwar Sharifai.
Meye manufar wannan aiki?
Malam Mubarak Abba shi ne jagoran matasan unguwar da ke jan ragamar aikin, ya ce, duba da matsalolin da suke fuskanta daga kwalbatin, waɗanda suka haɗa da yawaitar sauro da gurɓata muhalli tare a kyawun yanayi.
Ya ce, mun ɗauki wani mataki domin daƙile yaɗuwar cututtuka da rashin gyara magudanan ruwa kan haifar.
Unguwanni irin namu an saba ganin su, ba a tsari mai kyau ba, ta yadda muke saurin kamuwa da cututtuka waɗanda ke yaɗuwa nan da nan, amma yanzu idan muka kammala aikin ka ga za a samu sauƙi sosai.
Hakan ya sa bamu jira Gwamnati ba, mu kayi hoɓɓasa domin mu aiwatar da aikin.
Nawa za a kashe wajen kammala aikin?
Mubarak Abba yace, sun gudanar da ayyukan ci gaban unguwa da dama amma wannan shi ne mafi girma da suke yi.
Ana sa ran aikin zai lashe kuɗi har kimanin miliyan biyar.
Yadda ake samar da kuɗin aikin
Mutanen yankunan na tattara kuɗi-kuɗi a tsakaninsu inda kowa ke bada abin da Allah ya hore masa don gudanar da wannan aikin.
A cewar Muhsin Aminu Dukawa wanda ke tattara kudin aikin.
Iyaye mata na bada tasu gudummuwar
Iyaye mata ma ba a barsu a baya ba, wajen bada tasu gudummuwar.
Hajiya Fadima Danbalarabe wadda aka fi sani da Niniya tana cikin iyaye mata a yankin.
Ta ce, su na bayar da abinci ga masu aikin da sabulan wanke jiki da duk wani abu da Allah ya hore musu.
Yaya manyan unguwannin suka karɓi aikin?
Matasan da suka jagoranci aikin sun ce wannan aiki bai samu ba sai da gudummuwar masu unguwanni da dattijan yankin.
Alhaji Lamin Isah na cikin dattawan unguwannin, ya ce, wannan kwalabati ta daɗe tana ci musu tuwo a ƙwarya, amma yanzu ƴaƴansu sun tasamma magance musu matsalar ta.
Malaman Addini sun shigo cikin aikin
Da yake unguwannin sun yi shura da al’amuran addini ya sanya matasan suka sanya malaman addinin yankin kan gaba wajen gudanar da shi.
Gwani Hadi Sadisu Zangon Bare-bari fitaccen malamin alkur’ani ne a nan Kano wanda ke cikin wannan aiki.
Ya ce, yana farin ciki sosai yadda matasan unguwar suka neme shi matsayin mai bada shawarwari kan gudanar da aikin.
WANE TASIRI AIKIN ZAI YI GA KIWON LAFIYAR MUTANEN UNGUWANNIN?
Ibrahim Muhammad Dukawa, shi ne mataimakin Daraktan Lura da Lafiyar Muhalli na Ƙaramar Hukumar Birni Da Kewaye.
Ya ce, a matsayinsa na ɗan unguwar Dukawa sai da suka yi nazari kan dalilan samun cutar cizon sauro, da ɓarkewar annobar amai da gudawa a yankunansu.
Ya ci gaba da cewa, ko a yanzu an samu ragi sosai na yawaitar samun cutuka a yankin, duk da ba a kai ga ƙarasa aikin ba, kasancewar an rufe mafi yawa na kwalbatin.
A baya kafin wannan aiki, kusan kowane lokaci muna samun rahotannin amai da gudawa, dangane da sauro kuwa, yadda ka san duk Najeriya a nan ne, ake ƙyanƙyasar sauraye, saboda tsarin gine-ginen mu irin na cikin gari, ga kuma wannan kwalbati.
Muna sa ran idan an kammala wannan aiki, a samu sauyin gaske mai ɗorewa game da wannan al’amari.
Yaya sauran al’umma ke kallon aikin?
Masu kishin al’umma dai na cewa wannan shi ne abin da ya kamata al’umma su rika yi domin kawo ci gaba a yankunansu.
Alhaji Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Gwamnati Ikon Allah ɗaya ne cikin masu kishin al’umma a Kano.
“Muna kira ga sauran matasa da su yi koyi da waɗannan unguwanni saboda in an tsaya jiran gwamnati za a jima gyaran bai samu ba”.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum dai sun jima suna kalubalantar gwamnati kan yadda kusan kowacce unguwa ke fama da irin wannan matsaloli, kuma gwamnati ta kasa gyarawa har ta kai ga al’umma sun fara daukar irin wannan mataki na gyarawa da kansu.
Wannan rahoto ya samu tallafi daga Sol Solutions Journalism Network, USA da kuma Nigeria Health Watch.
You must be logged in to post a comment Login