Manyan Labarai
Rahoto: Kan dalilan da ya sanya ake yawan samu kisan kai a tsakanin ma’urata
Wani Malamin a sashen nazarin halayyar dan adam da ke Jami’ar Bayero a nan Kano Dr Sani Lawan Manumfashi, ya bayyana cewar yawaitar samun kisan kai musamman a tsakanin ma’aurata na da nasaba da damuwa da take yi wa mutane yawa, masamman ta bangaren rayuwar yau da kullum.
Dr Sani Manumfashi ya bayyana hakan ne bayan kammala shirin Barka da Hantsi nan Freedom Radiyo, da ya tattauna kan yadda ake samun yawaitar kasha kashe a cikin tsakanin ma’aurata a kwanan nan.
Ya kuma kara da cewar auratayya tsakanin mutane masu hali iri daya ma musamman masu saurin fushi, shi ma ya yana taka rawa wajan samun irin wadannan matsaloli a tsakanin ma’aurata.
Rahoto daga wakiliyar mu, Aisha Shehu Kabara na da ci gaban labarin.