Kiwon Lafiya
RAHOTO: Ranar yaki da cutar shan inna ta duniya
Daga Safara’u Tijjani Adam
Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ayyana ranar 24 ga watan Oktobar kowace shekara a matsayin ranar yaki da cutar shan inna.
Tun farko dai kungiyar Rotary International ce ta fara bijiro da bikin ranar a alif da dari tara da taminin da takwas, tare da bayyana cewa akwai yara dubu dari uku da hamsin da ke dauke da cutar.
A cewar hukumar lafiya ta duniya, cutar shan inna cuta ce da ke kama mutum dalilin wasu kwayoyin cututtuka da ke addabar garkuwar jikin dan adam.
Kuma kungiyar Rotary international ce ta fara bijiro da muhimmancin bikin ranar a alif da dari tara da tamanin da takwas, har ma ta ce yara sama da dubu dari uku da hamsin ne ke dauke da cutar.
Hakan ne ya sanya WHO ta ware ranar yaki da cutar domin fadakar da iyayen da basa bari a yiwa yaransu rigakafin cutar illar da ke tattare da hakan.
A wannan shekara ne dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce Najeriya afirka da ma duniya baki daya sun yi bankwana da cutar ta shan inna.
Ko a nan kano ma ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar da cewa jihar Kano babu mai dauke da cutar Polio kamar yadda kwamshinan lafiya na jihar Dr kabir Ibrahim Tsanyawa ya bayyana.
Dr Tijjani Husain shi ne shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano ya ce za su ci gaba da yin rigakafin cutar shan inna don tabbatar da an yake ta gaba daya.
Taken bikin ranar a bana shi ne: ‘baya da yanzu’ wanda ke bayyana irin halin da duniya ke ciki a baya lokacin da ake fama da cutar da kuma wannan lokaci da aka yi ban kwana da ita.
You must be logged in to post a comment Login